Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Batun dagewa Iran jerin takunkuman da Amurka ta kakaba mata da kuma dawowar Amurka a cikin yarjejeniyar ta 2015 su ne manyan ajandar tattaunawar.
A ranar 29 ga watan Nuwamba da ya gabata ne Iran da bangarorin suka koma bakin tattaunawar ta Vienna bayan tsaiko na watanni biyar.
Tattaunawar da aka soma a waccen lokacin ita ce irinta ta karkashin sabuwar gwamnatin shugaba Ibrahim Ra’isi.
A cikin shekarar 2018 ne tsohon shugaban kasar Donald, Trump, ya janye kasarsa daga cikin harjejeniyar tare da laftawa Iran jerin takunkuman karya tattalin arziki.
Ministan harkokin wajen aksar Iran, Hossein Amir-Abdollahian, ya bayyana a ranar Alhamis da ta gabata cewa Tehran na halartar tattaunawar da kyakyawar niyya, sannan ta dukufa wajen ganin an dage mata takunkumi, saidia hakan baya nufin za ta amince da wasu bukatu domin farantawa wasu rai.
342/